Kiwon Lafiya
Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta NECO ta saki sakamakon jarrabawar na bana
Hukumar shirya jarrabawar kammala makarantun sakandire ta kasa NECO ta saki sakamakon jarrabawar da daliban kasar nan suka rubuta tsakanin watan Yuni da Yulin bana.
A cewar hukumar ta NECO, sama da kaso 71 na daliban sun samu kiredit 5 da suka hadar da darusan Turanci da Lissafi.
Mukaddashin shugaban hukumar Abubakar Muhammad Gana ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a garin Minna, ya na mai cewa ci gaban da aka samu bai kai kaso daya cikin dari ba, idan aka kwatanta da shekarar bara.
Kamar yadda ya bayyana dalibai sama dubu dari 8 da 75 cikin miliyan daya da suka zauna jarrabawar sun samu kiredit 5 ciki babu darasin lisaffi dana turanci, inda kuma wadanda suka samu kiredit 5 da suka hadar da Turanci da Lissafi suka kai kaso 82 cikin dari.
Abubakar Muhammad Gana ya kuma ce akwai matsalolin satar Jarrabawa da suka samu sama da dubu 20, inda yace sun kama dalibai sama da dubu bakwai da suke satar amsa daga littattafai, inda ya ce an fi samun matsaloli a darasin Lissafi sama da kowanne darasi sai kuma darasin Turanci.