Kiwon Lafiya
Hukumar tsaro ta DSS ta sallami Yunusa Adamu Dan Gwani
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta sallami wani jigo a kungiyar siyasa ta Kwankwasiyya kuma tsohon kwamishinan ruwa Dakta Yunusa Adamu Dan-Gwani a daren jiya litinin bayan wattani uku da chafke shi.
Tsohon shugaban karamar hukumar Madobi Alhaji Sanusi Suraju Kwankwaso ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa da kamfanin jaridar Solacebase a yau Talata.
Ya kuma kara da cewa ana sa ran tsohon shugaban ma’aikatan a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso Dr.Yunusa Dangwani zai iso Kano a yau ko Gobe.
Alhaji Sanusi Suraju Kwankwaso ya ce za su ci gaba da bibiyar zargin da aka yi masa a gaban kotu har sai an kai magaryar tikewa.
Idan dai za’a iya tunawa a ranar 21 ga watan Maris ne hukumar ta DSS ta cahfke shi, Dan-Gwani a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a hanyar sa ta zuwa Kasar Saudi Arabiya don gudanar da aikin umrah.
Ana dai zargin sa da umarnin wani tsohon kyaftin din soja Umar Abdullahi mai ritaya da yada wata jita-jita da ke da alaka da mayakan Boko Haram da ya hadar da wani mamba a gidan gwamnatin jihar Kano.