Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Covid-19: Za mu fara rigakafi zagaye na 2 a ranar 10 ga Agusta – Buhari

Published

on

Kwamitin shugaban Kasa mai yaƙi da cutar COVID-19 ya ce, za a fara rigakafin zagaye na biyu a ranar 10 ga watan Agusta.

Daraktan yada labarai na kwamitin, Mista Willie Bassey ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a Abuja.

Bassey ya ce, rigakafin zagaye na biyu, yunkuri ne na yakar cutar da ta barke a karo na uku.

Gwamnatin Amurka ce ta bayar da alluran rigakafin samfurin Moderna sama da miliyan hudu, tun a ranar 1 ga watan Agusta, da za a yiwa wadanda suka fara daga shekaru 18 zuwa sama.

Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na yiwa mutane sama da miliyan 109 rigakafin cutar COVID-19 cikin shekaru biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!