Labarai
Ibtila’i: Fashewar tukunyar sinadarin masana’antu ta jikkata mutane sama da 30 a Kano
Sama mutane 30 ne suka jikkata kawo yanzu, sakamakon fashewar wata Tukunyar Sinadaran Masana’ntu mai guba a unguwar Shekar Maiɗaki, Mundaɗu da ke Kano.
Al’amarin ya faru ne a wani wajen sana’ar Ƴan Gwangwan da ke unguwar da misalin ƙarfe 3:45 na yammacin Jumu’a.
Mai unguwar Shekar Maiɗaki Malam Magaji Abdullahi ya tabbatarwa da Freedom Radio faruwar al’amarin.
Ya ce “An kirani da misalin ƙarfe 3:45 na yamma, an sanar dashi abu ya fashe a wajen da Saifullahi Muhammad ke sana’ar gwangwan”.
“Mutane da dama sun jikkata, mun kai sama da mutane 30 asibitin Ja’en sannan an tafi da wasu asibitin Murtala”.
Ya ƙara da cewa “Na sanar da ƴan sandan Ja’o’ji har sun tafi da wasu da ake zargi da hannu a ciki”.
A ziyarar da Freedom Radio ta kai unguwar ta iske jama’a sun fito wajen unguwar yayin da ake ta fita da wasu zuwa asibiti.
Mafi yawan waɗanda lamarin ya rutsa da su, mata ne da ƙananan yara, kamar yadda muka iske wasu daga ciki kwance a asibitin unguwar Ja’en.
Sai dai yawan mutanen da lamarin ya shafa sun zarce waɗanda asibitin na Ja’en zai iya ɗauka kamar yadda muka ganewa idonmu.
Mun kuma riski yadda da dama daga al’ummar yankin ke tserewa domin ceton ransu.
To amma koda Freedom Radio ta tuntuɓi hukumar kashe gobara ta Kano, ta ce bata samu rahoton faruwar al’amarin ba.
Yadda suke fara kamuwa da wannan cuta:
Wasu mazauna unguwar da muka zanta da su, sun ce waɗanda suka kamu da cutar na somawa ne da ƙaiƙayin maƙogaro.
Sai kuma tari da amai, har ma abin ya kai ga suma.
Unguwar dai na maƙotaka da kamfanunuwa abin da ya sanya da farko aka yi zargin ko warin sinadarin na fitowa ne daga kamfanunuwan.
You must be logged in to post a comment Login