Labaran Kano
ICPC ta horas da shugabannin kananan hukumomi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta bukaci shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano da su guji karkatar da akalar kudaden kananan hukumomin su zuwa wasu abubuwan na daban.
Shugaban hukumar anan Kano Alhaji Zayyanu Almu Dan Musa ne ya bayyana hakan, yayin wani taron nusar da shugabannin kananan hukumomi na kwanaki hudu da hukumar ta shirya a Kano.
Ya ce hukumar su ta mai da hankali a baya-bayannan wajen ganin shugabannin kananan hukumomin jihar, sun rika gudanar da ayyukan raya kasa da suka yi wa al’ummar su alkawari tun da fari kafin darewar su kan karagar Mulki.
Hukumar ICPC ta kwato kayayyakin aiki na naira miliyan 117 a hannun dan majalisar tarayya
Shugaba Buhari ya aika sunan Farfesa Bolaji Owasanoye a massayin shugaba hukumar ICPC
Zayyanu Almu Dan Musa ya kara da cewa, akwai bukatar shugabannin kananan hukumomi su san abubuwan da ake bukata daga bangaren su da kuma iyakar su wajen jagorancin al’umma, da hakan ba zai tabbata ba sai da irin wannan taron sanin makamar aiki da nusarwa.
Da yake jawabi tun da fari, Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Mutala Sule Garo, da ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Alhaji Sale Ado Minjibir, ya ce taron zai tallafa wajen kawo tsafta a ayyukan kananan hukumomin jihar Kano.
Wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomin da suka halarci taron, sun bayyana irin alfanun da suka samu, wanda shakka babu zai taimaka wajen bunkasa yanayin aikin su.
Wakilin mu Umar Idris Shuaibu da ya halarci taron da aka gudanar a nan Kano, ya ruwaito hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, ta sha alwashin ci gaba da wayar da kan shugabannin kananan hukumomi a kokarin da ake na rage yawaitar korafe korafe da suka shafi cin hanci da rashawa a sha’anin shugabancin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login