Kiwon Lafiya
ICPC:zata kwace wasu fulotai mallakar gidauniyar Shehu Musa ‘yar Adua
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta (ICPC) ta ce, za ta kwace wasu fulotai da gine-gine mallakin gidauniyar Shehu Musa Yar Adua da darajar kudin gine-ginen ya kai naira biliyan hudu da miliyan dari takwas.
Haka zalika ICP za ta kuma kwace wasu kadarorin guda ashirin da tara, mallakin gidauniyar ta Shehu ‘Yar Adua.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Mrs. Rasheedat Okoduwa jiya a Abuja.
A cewar sanarwar cikin kadarorin akwai fulotai da suka kai kusan shakta ashirin da uku da kuma wani gini da kuma wasu rukunan gidaje guda shida da ke Unguwar Wuse Zone one a Abuja.
Sanarwar hukumar ta ICPC ya bayyana cewa, binciken su na farko ya nuna cewa kadarorin mallakin gidauniyar Shehu ‘Yar Adua ne sai dai daga bisani sun musanta mallakar kadarorin kuma babu wanda ya bayyana kanshi a matsayin wanda ya mallaka.
Mrs Rasheedat Okoduwa ta cikin sanarwar dai ta kuma ce tun farko dama hukumar tattara haraji ta tarayya (FIRS) ce ta mika korafi kan cewa ma-mallakan kadarorin basa biyan haraji tsawon lokaci.