ilimi
Ilimi: Za mu tallafawa makarantun islamiyya da tsangayu a Kano – Ɗan-Zarga
Hukumar kula da makarantun islamiyya da na tsangaya a jihar Kano ta yi kira ga al’umma da su riƙa talafawa makarantun.
Hukumar ta buƙaci hakan musamman daga ɓangaren don bunƙasa ilimin addinin musulunci.
Shugaban hukumar Gwani Yahuza Ɗan-Zarga ne ya yi wannan kira jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki da gidauniyar Khalifa Dankade ta shirya da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Amurka a nan Kano.
“Da ma can abu ne da ya kamata ayi tun da daɗewa kuma munata kiraye kiraye ga ƙungiyoyin mu da su ɗauki gabarar yin wannan tsarin dan tallafawa makarantun mu na addini da kuma islamiyya duba da cewa suma suna buƙatar tallafi”.
Maƙa sudin taron dai shi ne tattaro dukkanin masu ruwa da tsaki don tattaunawa tare da samo mafita kan sha’anin ilimin addini.
Gidauniyar za ta tallafawa tsangayu sittin a jihohi shida na arewacin Ƙasar nan a matsayin gwaji, har na tsawon shekara guda.
You must be logged in to post a comment Login