Connect with us

Kiwon Lafiya

Covid-19: Gwamnatin Kano ta bada umarnin rufe makarantun Allo dana Islamiyya

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe dukkan Tsangayun karatun alkur’ani da makarantun Islamiyya dake fadin jihar don kaucewa annobar Coronavirus.

Shugaban hukumar Tsangayu da makarantun allo ta jihar Kano Gwani Yahuza Dan Zarga ne ya bayyana hakan kamar yadda jaridar Solacebase ta rawaito.

Gwani Dan Zarga ya ce za a rufe makarantun daga ranar Litinin 23 ga watan Maris da muke ciki, kuma hakan ya biyo bayan cimma matsayar da gwamnonin arewa maso yammacin kasar nan su kayi ta rufe dukkan makarantu a yankin.

Idan baku manta ba, a ranar Alhamis ne gwamnonin jihohin Arewa maso yammacin kasar nan suka amince a rufe makarantun yankin domin takaita cudanyar jama’a da dama, wanda hakan ka iya taka rawa wajen yaduwar cutar Coronavirus.

Karin labarai:

Covid-19: An fara rufe makarantun Islamiyya a Kano

Covid-19: An dakatar da kwallon kafa a Kano saboda Coronavirus

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,801 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!