Labarai
Atiku ya koka kan tura kudi asusun sa ba tare da sanin sa ba

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa bayan an tura kuɗi zuwa asusun ajiyarsa na sirri ba tare da saninsa ko amincewarsa ba.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce mutumin da ya tura kuɗin ba a san shi ba, kuma ya rubuta “Contribution Electioneering Campaign,” ma’ana “Gudunmawar Kamfen ɗin Zaɓe.”
Atiku ya ce shi da tawagarsa ba su nemi ko amince da irin wannan gudunmawa ba, yana mai cewa abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda aka samu bayanan asusun nasa na sirri, duk da cewa ba a bayyana su ga jama’a ba.
Ya ce idan har bayanan asusun sirrin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa za su iya shiga hannun wasu ba tare da izini ba, hakan na nuna cewa sirrin bayanan kuɗin kowane ɗan kasa na cikin haɗari.
You must be logged in to post a comment Login