Labarai
Ina buƙatar sanin shari’o’i masu cin karo da juna da aka gudanar – CJN Tanko Muhammad
Babban jojin ƙasa mai shari’a Tanko Muhmmad ya buƙaci a gabatar masa da bayanan hukunce-hukuncen shari’o’i masu cin karo da juna da aka zarta a kotunan ƙasar nan.
Mai magana da yawun hukumar sharia ta ƙasa Soji Oye ne ya tabbatar da hakan.
Soji Oye ya ce, manyan alƙalan jihohin Rivers, Kebbi, Cross Rivers, Anambra, Jigawa da Imo za su gana babban Jojin a Litinin ɗin nan.
A cewar sa, za su gana ne domin amsa tambayoyi kan umarni kotu na wasu shari’o’i masu rikitarwa da aka bayar a jihohin su daban daban.
Wannan ya biyo bayan yadda aka samu rikice-rikicen cikin gida a manyan jam’iyyun siyasar ƙasar nan a baya-bayan nan.
You must be logged in to post a comment Login