Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya bukaci majalisa ta tabbatar da sunayen da ya aike mata

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci majalisar dattawa da ta tabbatar da nadin mutane 12 da aka zaba a matsayin mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin arewa maso gabashin kasar nan wato NEDC.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu, ya fitar jiya Juma’a a Abuja, yace ‘bukatar shugaban kasar na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan mai kwanan watan 3 ga watan nan da muke ciki’.

“Wadanda aka nada sun hada da: Bashir Bukar Baale, Shugaban da Suwaiba Idris Baba, da Musa Yashi, da Dakta Ismaila Maksha da Umar Hashidu”.

“Sauran sun hada da Mustapha Ahmed Ibrahim da Hadiza Maina da Grema Ali da Onyeka Bishara-Tony da Uwargida Hailmary Ogolo Aipoh, da kuma Air Commodore Babatunde Akanbi mai ritaya”.

 

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!