Labarai
Inda ba ƙasa: Za a fara gasar zabga Mari a Najeriya
Shugaban kamfanin tsara wasanni na ƙasa ya ce za a fara gasar zabga Mari a Najeriya.
Masu shirya sabuwar gasar da za a fara a karon farko a Najeriya, sun ce za a fara gasar Marin ne cikin watan Oktoba.
Babban Daraktan kamfanin tsara wasannin na TKK Sports, Abdulrahman Orosanya ne ya bayyana haka, ranar Juma’a a Lagos.
Orosanya ya ce, ba a sa ranar da za a fara gasar ba amma ana sa ran farawar a cikin watan Oktoba nan da muke ciki, wanda kuma za’a ƙarkare a cikin watan Disambar shekarar, tare da ba da kyautar Kofuna ga zakarun da suka lashe gasar.
An dai ƙirƙiri wannan wasan ne a ƙasar Rasha, amma ƙasar Amurka da ragowar ƙasashen Turai su ka zamanantar da ita, inda a yanzu ake gudanar da gasar a Burtaniya, Poland da Afrika ta Kudu da sauransu.
Kazalika an tsara gasar abisa mataki-mataki wanda ya haɗa da na matakin ramammun mutane, tsaka-tsaki, ƙarti, sai kuma na jibga-jibgan ƙarti.
Kuma ana yin galaba ne idan an gaurawa mutum Mari ya kife ƙasa ko ya nuna an fi ƙarfin sa, kuma duk Inda gwanaye biyu su ka nuna dauriya da jarunta, to alƙalin wasa ne zai yanke hukunci wanda kafin lokacin fara gasar za’a horar da su da kuma ƴan takarkarun gasar.
You must be logged in to post a comment Login