Connect with us

Labarai

INEC ta amince da tsawaita wa’adin ci gaba da rajistar katin zabe

Published

on

Hukumar zabe ta Kasa INEC, ta amince da tsawaita wa’adin ci gaba da rajistar masu kada kuri’a (CVR) da karin makwanni biyu. 

 

A baya dai an tsara kammala rijistar ne a ranar 10 ga watan Yuli, 2026, amma hukumar ta ce yanzu za a ci gaba da yin rijistar har zuwa ranar 24 ga watan na Yuli.

 

Hukumar ta bayyana cewa ta dauki wannan mataki ne bayan bukatar da dimbin ‘yan Najeriya masu cancantar kada kuri’a suka gabatar, domin ba wa karin mutane damar yin rajista da kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa damar shiga cikin kundin masu kada kuri’a kafin zabuka masu zuwa.

 

INEC ta ce wannan tsawaitawa na nuna kudirinta na tabbatar da cewa duk wani dan Najeriya da ya cika sharuddan yin zabe ya samu dama cikin sauki wajen yin rajista, domin karfafa tsarin dimokuradiyya da kuma fadada shigar al’umma cikin harkokin zabe a fadin kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!