Labarai
Mambobin NUT sun hana Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati shiga dakin taro

Malaman makarantun firamare da sakandare a birnin tarayya Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT, sun hana Shugaban Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta birnin Emeka Ezeh, shiga dakin taro domin yi wa ma’aikatan gwamnati da ke jiran fara jarabawar karin girma ta shekarar 2025 jawabi.
Jaridar DailyTrust, ruwaito cewa, dubban malamai daga ƙananan hukumomi shida na na birnin tarayyar ƙarƙashin jagorancin Shugaban NUT na na birnin Abdullahi Mohammed Shafas, da Babbar Sakatare, Margareth F. Jethro, sun taru a ƙofar dakin taro na Jami’ar National Open University of Nigeria NOUN da ke kan titin Kubwa a Abuja.
Emeka Ezeh, wanda ya isa wurin da misalin ƙarfe 8:12 na safe tare da rakiyar jami’an ‘yan sanda masu ɗauke da makamai, ya yi ƙoƙarin shiga domin yi wa ma’aikatan jawabi kafin fara jarabawar, amma malaman suka hana shi shiga.
You must be logged in to post a comment Login