Labarai
Dole EFCC da DSS su faɗaɗa bincike kan zargin kafa hukumar bogi – Temitope Ajayi

Ɗaya daga cikin hadiman Shugaba Bola Tinubu, Temitope Ajayi, ya yi kira ga Hukumar EFCC da DSS da kuma Rundunar Ƴansanda su faɗaɗa bincike kan zargin kafa wata hukumar bogi, tare da gano waɗanda suka taimaka wa wanda ke ikirarin shugabantar hukumar Adeyemi Adeniyi Matthew.
A cewarsa, akwai yiwuwar wasu daga cikin jami’an gwamnati sun taka rawa a lamarin, kuma suna ƙoƙarin jefa zargi kan shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.
Lamarin ya biyo bayan iƙirarin da Prince Adeniyi Adeyemi ya yi cewa Shugaba Tinubu ya naɗa shi shugaban wata hukuma mai suna Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Shawarwarin Tattalin Arziki.
Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta bakin Femi Gbajabiamila da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, sun musanta hakan, tare da cewa gwamnatin tarayya ba ta da irin wannan hukuma.
You must be logged in to post a comment Login