Labarai
INEC ta bukaci kotun sauraron korafin zabe ta sauya damar da ta bai wa Atiku da Peter Obi
Hukumar INEC ta bukaci kotun da ke sauraren korafin zaben shugaban kasa da ta sauya izinin da aka bai wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi na jam’iyyar Labour na nazartar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben shugaban kasa a bana.
A wani kudiri da ta fitar a ranar 4 ga wannan watan da muke ciki na Maris, hukumar INEC ta yi fatan kotun za ta sauya umarnin wucin-gadi da ke hana ta taba kayayyakin zaben, tana mai cewa akwai bukatar ta sake seta na’urar BVAS domin gudanar da zaben gwamnoni da za a gudanar a Asabar mai zuwa.
A ranar 3 ga watan nan na Maris ne dai kotun daukaka kara ta bai wa Atiku Abubakar da Peter Obi damar nazartar na’urar BVAS da INEC ta yi amfani da ita a zaben shugaban kasa ranar 25 ga watan jiya na Faburairu.
Kotun ta hana INEC tu’ammali da na’urar har sai ‘yan takarar biyu sun gudanar da binciken kwa-kwaf a cikinta biyo bayan zargin da suka yi na yi musu magudi a zaben.
You must be logged in to post a comment Login