Labarai
Shugaba Tinubu na shirin gabatar wa majalisar sun tarayya kasafin 2027

Shugaban kasa, Bola Tinubu, zai gabatar wa majalisar sun tarayya kasafin kuɗin shekarar 2027 kafin ƙarshen shekarar da muke ciki.
Ƙaramar ministar kasafin kudin ƙasar, Dakta Doris Anite-Uzoka ce ta bayyana haka a wani taron manema labarai a fadar gwamnatin da ke Abuja, jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswar da Shugaba Tinubu ya jagoranta.
Dakta Doris ta ce sun fara aikin shirya kasafin kuɗin shekarar 2027, kuma manufarsu ita ce a gabatar da shi kafin ƙarshen shekara.
Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan Ofishin Kasafi na Tarayya, a cikin wata takardar kira Kan kasafin kuɗaɗen ma’aikata mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Satumbar 2026, wadda Darakta Janar na Ofishin Kasafin Kuɗi, Tanimu Yakubu, ya sanya wa hannu,
Tanimu Yakubu,ya kuma umarci dukkan ma’aikatu,da hukumomin gwamnati su gabatar da shawarwarinsu na kuɗaɗen ma’aikata na shekarar 2027, tare da dokokin da suka kafa su.
Takardar ta wajabta wa ma’aikatu, sassa da hukumomin gwamnati su haɗa dokokin da suka kafa su da shawarwarin da suke gabatarwa, wani sabon sharaɗi da aka ƙirƙira bayan badaƙalar hukumomin bogi da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa (ICPC) ta gano.
You must be logged in to post a comment Login