Connect with us

Labarai

INEC ta fitar da sunayen ‘yan takarar Shugaban Kasa a 2027

Published

on

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi, na cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

INEC ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar shugaban ƙasa 18 da mataimakansu, inda Tinubu zai tsaya takara karkashin jam’iyyar APC tare da Kashim Shettima, Atiku na jam’iyyar ADC tare da Rotimi Amaechi, yayin da Peter Obi na jam’iyyar NDC zai yi takara tare da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.

Jerin ya kuma kunshi ɗan takarar jam’iyyar AAC Omoyele Sowore da na PDP Sandy Onor, yayin da jam’iyyar Labour Party ke tsayawa da Sunday Okereke. Haka kuma, INEC ta cire jam’iyyar NNPP daga jerin, bayan ɗan takararta Dikwa Mohammed bai bayyana a jerin na ƙarshe ba.

Zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya an tsara gudanar da su ne a ranar 16 ga Janairun 2027. Fitar da wannan jerin na ƙarshe na nufin INEC ta kammala tabbatar da ‘yan takarar da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!