Labarai
Obi da Kwankwaso sun nemi a yi adalci kan kisan Danshagamu a Kano

Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun yi Allah-wadai da kisan mai sharhi kan harkokin siyasa a Kano, Ibrahim Khalil Danshagamu, tare da neman a hukunta waɗanda suka aikata laifin.
A saƙonnin ta’aziyyarsu daban-daban, jagororin siyasar sun buƙaci gwamnatin Kano da hukumomin tsaro su gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
Danshagamu ya rasu bayan an kai masa hari da makami mai kaifi a gidansa da ke unguwar Gaida, Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Rundunar ’yan sandan Kano ta ce ta kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan.
Peter Obi ya ce bambancin ra’ayi ko suka ba zai taɓa zama hujjar amfani da tashin hankali ba, yana mai jaddada muhimmancin kare ’yancin faɗar albarkacin baki.
You must be logged in to post a comment Login