Labarai
Inganta tsaro a filayen wasanni zai kawo karshen shaye-shaye a Kano – Dagaci
Dagacin Sharada Alhaji Ilyasu Mu’azu ya shawarci gwamnati kan ta kara yawan ma’aikata dake kula da filin wasanni na kofar Na’isa don samar da tsaro da kawo karshen matsalar sayar da miyagun kwayoyi musamman a unguwannin dake makotaka da filin.
Alhaji Ilyasu Mu’az ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai, yana mai cewa sun dauki matakin ganawa da masu irin wannan sana’ar ta sayar da kwayoyi a unguwar domin nema musu makoma ta hanyar basu jari don su dogara da kansu.
Dagacin na unguwar Sharada ya kara da cewa suna sake kira ga masu gudanar da sana’ar sayar da kayan maye ga ‘ya’yan jama’a da su sake tunani su kuma dawo domin a nema musu makoma domin su tsira a wajen haliccinsu kasancewar suna cutar da al’umma.
Rubutu masu alaka :
Da mu za’a kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi –ALGON
Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar yaki da shaye-shayen kayan maye
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito dagacin na unguwar sharada Alhaji Ilyasu na shawartar jami’an tsaro da suji tsoran Allah a cikin ayyukansu musamman wajen ganin an hukunta duk wanda aka kama da aikata laifi.
You must be logged in to post a comment Login