Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Inter Milan ta nada sabon mai horaswa

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan ta nada Simone Inzaghi a matsayin mai horas da ‘yan wasan kungiyar bayan ficewar Antonio Conte daga kungiyar.

Inzaghi mai shekara 45 ya sanya hannu a yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu da kungiyar.

Inzaghi dai ya ki amincewa ne da sabunta kwantiraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Lazio bayan karewar kwantiragin a makon jiya.

Takwas daga cikin manyan kungiyoyi goma dake fafatawa a gasar Serie A sun canja masu horaswa tun a karshen kakar wasannin da ta gabata.

Antonio Conte ya bar Inter Milan ne a watan Mayun 2021 yayin da ya rage shekara guda kafin kwantiraginsa ya kare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!