Ƙetare
Iran ta kai harin martani kan sansanonin Amurka

Iran ta ce dakarun juyin juya halin ƙasar (IRGC) sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya da makamai masu linzami na rundunar sararin samaniyarta.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa sashen hulɗa da jama’a na IRGC ya bayyana cewa harin ya zo ne a matsayin martani ga abin da ya kira “ta’addancin soji” da Amurka ta aiwatar a Sirik da tsibirin Qeshm na Iran.
A cewar sanarwar, an kai hare-haren ne kan sansanonin da Iran ta bayyana a matsayin na “abokan gaba” da ke yankin da makamai masu linzami.
Rahotanni sun ce Iran ta zargi Amurka da kai hari kan wani hasumiyar sadarwa a kudancin tsibirin Qeshm, lamarin da ya haddasa wannan martani daga Tehran.
Sai dai rundunar CENTCOM ta Amurka ta bayyana hare-haren da ta kai a yankin a matsayin matakan kariyar kai, yayin da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da ƙara tsananta duk da ƙoƙarin sasanta rikicin.
You must be logged in to post a comment Login