Labarai
Sojin ruwan Amurka sun kwace jirgin Ruwa ɗauke da ɗanyen mai na dala biliyan 1.05 mallakin Iran

Wani shafin intanet da ya kware wajen bibiyar jiragen ruwan ƙasashen duniya, ya ce hotunan tauraron Dan adam ya nuna yadda wani jirgi mai ɗauke da ɗanyen mai da ya kai darajar dala biliyan 1.05 da ke kan hanyar komawarsa Iran, sojin ruwan Amurka sun kwace shi.
Masu bibiyar tankokin dakon mai a tekun, sun ƙara da wallafa cewa masu gadin teku sun kwace wani jirgin Iran mai ɗauke da man da ya kai darajar dala miliyan 380 a tekun India, kuma yanzu kamar an karkatar da shi Amurka.
Har yanzu dai babu cikakkiyar hanyar safarar ɗanyen mai a cikin tekun Gulf, ko kuma babu wani tabbas cewa jirgi zai kai inda ya nufa kalau.
You must be logged in to post a comment Login