Connect with us

Labarai

SSANU ta bayyana shirin ta na tsunduma yajin aiki na sai baba ta gani

Published

on

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i ta kasa SSANU ta bayyana shirin ta na shiga yajin aikin sai baba ta gani, yayin da wa’adin ranar 30 ga watan Afrilu na kammala sabunta yarjejeniya da gwamnatin tarayya ke karatowa.

 

Kungiyar ta ce har yanzu ba a cimma matsaya ba a tattaunawar da ake yi da gwamnati, lamarin da ke barazana ga ci gaba da ayyukan jami’o’i a faɗin kasar nan.

 

SSANU ta ce idan aka kai ranar ba tare da samun cikakkiyar matsaya ba, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen fara yajin aikin domin neman hakkokin mambobinta.

 

Haka kuma ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan da suka dace domin kaucewa tsaikon karatu da yajin aikin da ka iya shafar dalibai da harkokin ilimi baki daya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!