Connect with us

Ƙetare

An amince da tsagaita wuta a Labanon bayan hare-haren Isra’ila

Published

on

Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah sun amince da tsagaita wuta a Lebanon bayan wani harin da aka kai cikin dare wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane aƙalla 47, a cewar ma’aikatar lafiya.

Isra’ila ta ce hare-haren na mayar da martani kan ayyukan ƙungiyar Hezbolah, ciki har da wani harin da aka kai cikin dare wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Isra’ila huɗu.

Tsagaita wutar ta fara aiki ne da ƙarfe 16:00 agogon ƙasar amma ƴan wakilan mu da ke ƙasa sun ce anci a gaba da kai hare-hare.

Wannan dai wani gwaji ne na yarjejeniyar da Amurka da Iran suka ƙulla a farkon wannan makon, wadda ta buƙaci a dakatar ayyukan soji a dukkan fagen daga da suka haɗa da Lebanon.

Rundunar IDF dai ta sha alwashin “ci gaba da kawar da duk wata barazana nan take” da kuma “mai da martani kan duk wani abu da Hezbollah ta aikata”.

A halin da ake ciki, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani saɓa alƙawari da Isra’ila ta yi “za a rataya wa Amurka alhakinsa”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!