Labaran Kano
Iyaye su tabbata ‘ya’yan su na amfani da takunkumin rufe hanci – Adamu
Kungiyar masu makarantu masu zaman kansu ta kasa reshen jihar Kano, ta bukaci iyayen yara da su tabbatar ‘ya’yansu sun je makaranta sanye da takunkumin rufe hanci da baki.
Shugaban kungiyar Muhammadu Malam Adamu ne ya bayyana haka, yayin wata ziyara da kungiyar ta kaiwa hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano.
“Ya ce tuni makarantu masu zaman kansu a jihar Kano suka kammala shirye-shirye don kare lafiyar dalibai da malamai daga cutar Corona”.
Da ya ke mayar da jawabi shugaban hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano Musa Abba Dan-Kawu, ya bukaci makarantu masu zaman kansu da su tabbatar sun yi rajistar daukar bayanan ko wace makaranta da hukumar ta ke yi ta intanet don ci gaban harkokin ilimi a jihar Kano.
Shugaban kwamitin amintattu na uwar kungiyar ta kasa, Toseb Mijinyawa, “Ya ce sun kai ziyarar ne don yabawa hukumar, sakamakon hadin kan da ta ke ba su wajen gudanar da makarantunsu”.
You must be logged in to post a comment Login