Connect with us

Labaran Kano

Kano ta kulla kawance da Fashanu don bunkasa harkokin wasanni

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kulla kawance da tsohon dan wasan Najeriya wanda kuma ya ke buga wa kasar Ingila wasa John Fashanu, domin ciyar da harkokin wasanni gaba a jihar.

An dai kulla kawancen ne yayin da Fashanu ya kawo ziyara a nan jihar Kano a karshen makon jiya.

Fashanu ya bayyana jihar Kano a matsayin matattarar zakakuran ‘yan wasa masu tasowa.

Yayin da yake tattaunawa da mataimakin gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a ofishin sa, tsohon dan wasan ya ce, ya zo Kano ne don tattauna shirye-shirye a yunkurin sa na kafa sabuwar makarantar koyar da harkokin wasanni tare da hadin kan gwamnatin jihar ta Kano.

Ya ce ”All…. ya albarkaci Kano da matasa da suka iya kallon kafa wadan da idan suka samu koyarwa da kuma horon da ya dace dasu, to babu shakka za a yi alfahari dasu a nan gaba.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Archives