Labarai
JAMB ta saki sakamakon ɗalibai 279 da ta rike kan zargin magudi

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta Najeriya JAMB, ta saki sakamakon dalibai 279 na jarabawar UTME da ta rike domin ci gaba da bincike kan zargin magudi.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a yau Alhamis a shafinsa na X, inda ya ce an saki sakamakon ne bayan cikakken bincike da hukumar ta gudanar.
Ya ce an soke wasu sakamakon daliban da aka tabbatar da samun hujjar aikata magudi a kansu, yayin da aka saki na wasu bayan hukumar ta gano babu wata kwakkwarar shaida da ke nuna sun yi laifi.
JAMB ta bukaci daliban da har yanzu ba su ga sakamakonsu ba da su tura sakon “UTMERESULT” zuwa 55019 ko 66019 ta layin wayar da suka yi rajista da shi domin duba matsayinsu.
You must be logged in to post a comment Login