Labarai
Mun ƙara tsaurara tsaro don hana shigowar masu ɗauke da Ebola- FAAN

Hukumar Kula da Filayen Jiragen saman Najeriya FAAN, ta ce ta kara tsaurara matakan kariya a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa sakamakon sake bullar cutar Ebola a wasu sassan tsakiyar Afirka.
Daraktan Hulda da Jama’a da kare hakkin fasinjoji na hukumar, Henry Agbebire, ne ya bayyana hakan inda ya ce, FAAN na aiki kafada da kafada da Ma’aikatar Kula da Lafiya ta Filayen Jiragen Sama da Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta kasa NCDC, domin kara sa ido kan fasinjoji musamman masu shigowa daga yankunan da ake fargabar yaduwar cutar.
A cewar hukumar, ana gudanar da bincike kan fasinjoji domin gano alamomin cutar Ebola, yayin da duk wanda ake zargi zai fuskanci killacewa tare da karin gwaje-gwaje kamar yadda dokokin lafiya na kasa da kasa suka tanada.
Wannan dai na zuwa ne bayan sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, tare da rahotannin cewa cutar ta bazu zuwa kasar Uganda.
You must be logged in to post a comment Login