Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jami’an Civil Defence sun cafke matashin da ya yi yunƙiurin shiga ɗakin kwannan ɗalibai mata

Published

on

Rundunar tsaro ta Civil Defense shiyyar Kano, ta kama wani matashi da ake zarginsa da yin ɓadda kama ta hanyar yin shigar mata yana ƙoƙarin shiga dakin kwanan ɗalibai a wata jami’a mai zaman kanta da ke tsakiyar birnin na Kano da tsakar dare.

Mai magana da yawun rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, an kama wanda ake zargin ne mai suna Muhammad Munzali mai kimanin shekaru 35 ɗan asalin karamar hukumar Shanono a dai-dai lokacin da ya ke kokarin shiga dakin kwanciyar matan.

Sai dai yayin amsa tambayoyi wanda ake zargin ya ce ba da saninsa ya shiga wurin ba, ya zata wani Otal ne.

Daga bisani rundunar tsaron ta Civil Defence, ta ce wanda ake zargin na tsare a hannunsu suna ci gaba da gudanar da bincike domin daukar mataki na gaba kansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!