Kaduna
Jami’ar Ahmadu Bello ta kirkiro irin masara da ke jure fari, tsutsotsi da kwari
Hukumar bunkasa fasahar bin hanyoyin kimiyya wajen inganta rayuwar abubuwa masu rai (National Biotechnology Development Agency), ta ce, samar da sabon irin masara mai suna Tela Maize da Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari’a ta yi, zai taimaka gaya wajen samar da isash-shen masara a kasar nan.
Shugaban hukumar farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da cibiyar bincike kan harkokin noma ta Jami’ar Ahmadu Bello ta gudanar game da sabon nau’in irin masaran a ranar talata a Zari’a.
Farfesa Abdullahi Mustapha, ya ce, manoma a Najeriya za su samu alfanu mai yawa sakamakon irin masaran Tela MAIZE da ya ce yana da ingancin da zai cike gibin da kasar nan ke da shi a bangaren noman masara.
Ya kuma kalubalanci masu sukar amfani da hanyoyin kimiyya wajen inganta rayuwar abubuwa masu rayuwa, yana mai cewa, idan suna da hujjoji da suka nuna karara akwai illa kan cin nau’in abinci da aka ingantashi ta hanyoyin kimiyya, to su gaggauta gabatar da hakan, domin hukumar a shirye ta ke ta dauki shawarwarin jama’a don kyautata ayyukanta.
A nasa bangaren farfesa Rabi’u Adamu wanda shi ne jagoran masana kimiyyar da su ka yi aikin samar da sabon irin masaran na Tela Maize, ya ce, nan ba da jimawa ba, cibiyar za ta fitar da sabon irin don amfanin manoma.
‘‘A yanzu Najeriya tana da gibin tan miliyan shida na masara saboda haka ina tabbatar muku wannan sabon irin da muka kirkiro na‘Tela Maize’ zai cike wannan gibi’’ inji farfesa Rabi’u S. Adamu
Mista Yarama Ndirpaya babban jami’I ne a majalisar bunkasa harkokin noma ta kasa, ya shawarci manoma da su yi amfani da damar da su ka samu wajen amfani da sabon irin wanda ya ce zai samar musu da yabanya mai yawa.
You must be logged in to post a comment Login