Labaran Kano
Jami’ar Bayero ta ringa la’akari da daliban jihohi don basu guraban karatu – Sarkin Kano
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya shawarci hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero da ke nan Kano, ta riga la’akari da yawan daliban Jihohi da ke neman gurbin karatu Jami’ar wajen daukansu.
Alhaji Aminu Ado Baeyro ya bayyana hakan ne lokacin karbar bakuncin hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero, a karkashin sabon shugabanta, Ferfesa Abbas Saggir Adamu a fadarsa.
Sarkin ya bukaci sabon shugaban Jami’ar da ya riga kwaikwayon irin salon shugabannin baya domin dora daga inda suka tsaya don bunksa ilimi a Jami’ar.
A nasa bangaren, sabon shugaban Jami’ar ta Bayero Ferfesa Abbas Sagir Adamu, ya ce sun zo fadar ne domin gabatar da kansa a matsayin sabon shugaban Jami’ar da sauran manyan Jami’ai na Jami’ar baya ga sanar da martaba sarki Kano kadan daga cikin manufofinsu na ciyar da Jami’ar gaba.
Wani labarin kuma, gidauniyar Panacea mai rajin kauda aukuwar Hamada da dasa bishiyu ta kasa, karkashin jagorancin shugaban kungiyar Dahiru Muhammad Hashim, y ace, sun kai ziyarace ga mai martaba sarkin Kano a fadarsa, inda shugaban ya yi Karin haske gamida muhimmancin dasa bishiyu don inganta Muhalli.
Wakilinmu Muhammad Harisu Kofar Nassarwa ya ruwaito cewa, shugaban gidauniyar Dahiru Hashim ya bukaci al’umma da su riga dasa bishiyu a inda ya kamata domin kaucewar barazanar Hamada.
You must be logged in to post a comment Login