Labarai
Jami’ar FUD ta Jigawa ta nemi haɗin kan ’Yan Sanda domin dakile ƙungiyoyin asiri a makarantar

Jami’ar Tarayya da ke Dutse a Jihar Jigawa, ta nemi haɗin kan Rundunar ’Yan Sandan jihar domin dakile tashe-tashen hankula da ayyukan ƙungiyoyin asiri da ake zargen wasu ɗalibai da aikatawa
Jami’ar ta bayyana hakan ne yayin ziyarar ban-girma da Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Muhammad Gumel, tare da shugabannin jami’ar da wasu ma’aikata suka kai wa sabon Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, Tijjani Murtala, a hedikwatar rundunar da ke Dutse.
Farfesa Gumel ya ce haɗin gwiwa tsakanin jami’ar da ’yan sanda na da muhimmanci wajen musayar bayanan sirri, dakile aikata laifuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma nuna damuwa kan bullar wasu ayyukan ƙungiyoyin asiri da sauran munanan ɗabi’u a tsakanin wasu ɗaliban jami’ar, yana mai cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa kafin lamarin ya yi kamari.
A nasa martanin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jigawa, Tijjani Murtala, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da jami’ar domin tabbatar da tsaron ɗalibai da ma’aikata.
Rundunar ta kuma yi alkawarin ƙara sintiri, sanya jami’an tsaro a wuraren da suka dace, tattara bayanan sirri da ɗaukar wasu matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a jami’ar da kewayenta.
You must be logged in to post a comment Login