Labarai
Hukumar ICPC ta gano wasu ma’aikatan bogi guda 900

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC ta ce ta gano wasu hanyoyin damfarar albashin gwamnati, ciki har da wani jami’in da ya saka mutane 14 daga cikin iyalinsa cikin jerin ma’aikatan gwamnati.
Shugaban hukumar, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan a Abuja, ya ce a wani bincike da hukumar ta gudanar, an kuma gano wani mutum da ya saka sunan matarsa,da yaransa huda biyu mace da namiji,da wasu ‘yan uwansa cikin tsarin albashin gwamnati, inda shi kaɗai yake karɓar albashin mutane 13.
Shugaban ya kuma ce hukumar ta gano kusan ma’aikatan bogi 900, bayan gudanar da bincike na tsawon shekara guda, tare da samun umarnin kotu kan wasu daga cikinsu.
Ya kuma bayyana cewa a shekarar 2024, hukumar ta kwato sama da Naira biliyan 24 da ake zargin sun shafi kuɗaɗen fansho na ma’aikatan bogi.
You must be logged in to post a comment Login