Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa matatun man kasar nan za su koma aiki

Published

on

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa matatun man kasar nan za su koma aiki, inda ya ce gwamnati na sake tsara yadda za a tafiyar da su domin su samar da riba da amfani ga ƙasa.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar dallalan man fetur NUPENG a Fadar sa dake birnin tarayya Abuja.

 

Ya ce kasancewar matatar suna aiki ba yana nufin tana aiki yadda ya kamata, ya kuma ce gwamnati zata cigaba da sanya indo dan ganin an samar da riba da amfanin da aka gina ta a kai.

 

Shugaban Kungiyar, Salimon Oladiti, ya kuma roƙi Tinubu da ya kawo ƙarshen ɗaukar ma’aikatan wucin gadi a ɓangaren man fetur da iskar gas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!