Labarai
Jami’ar Aliko Dangote ta ce za ta bude sashin koyar da fasahar hada magunguna da Kere Kere.

Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote dake garin Wudil, ta ce nan bada jimawa ba za ta bude sashin koyar da fasahar harhada magunguna da kuma Kere kere a Jami’ar.
Shugaban Jami’ar Farfesa Musa Tukur Yakasai ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye daliban Jami’ar karo na biyar dake gudana.
Ya kuma ce, Jami’ar tana ci gaba da samun sahalewar hukumar kula da Jami’o’i ta Kasa NUC domin cigaba da inganta harkokin Ilimi a Jami’ar.
Da yake jawabi shugaban gudanarwar Jami’ar ta Aliko Dangote mai shari’a Abdu Aboki ya ce Jami’ar na kokari wajen ganin an yaye dalibai masu tarbiyya, hakan tasa ba sa yadda a aikata duk wani abu na rashin tarbiyyaba a makarantar.
You must be logged in to post a comment Login