Labarai
Jami’in KAROTA ne ya haifar da hatsarin Kano Club – Ƴan Sanda
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, jami’in hukumar KAROTA ne ya haifar da hatsarin mota a shatale-talen Kano Club.
Mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Ɗan Sanda Abokin Kowa na nan Freedom Radio.
Kiyawa ya ce, rahotannin da suka samu ya nuna cewa, mai adaidaita sahu ne ya taho daga kan gada zai wuce shatale-talen.
Amma a kan hanyar sa sai wani jami’in KAROTA ya tsare shi da sanda har ya bigi adaidaita sahun sa, lamarin da ya sanya ya tsorata har ya yi ƙoƙarin canja hanya don kada a ƙara dukar masa Adaidaita.
A daidai wannan lokaci ne kuma wata mota ta taho, ta kuma doki adaidaita sahun, wanda akwai wani fasinja a ciki Aliyu Sani ɗan unguwar Ƙofar Ruwa mai shekaru 27 wanda ya bugu a kan sa, a cewar sa.
DSP. Kiyawa ya ce, ƴan sanda sun kai shi asibitin ƙwararru na Murtala inda a nan likitoci suka tabbatar ya rasa ransa.
Ko da aka tambaye shi yanzu ina matsayar jami’an KAROTAn da ake zargi sun haifar da afkuwar wannan hatsari, sai ya ce, ai tuni Kwamishinan ƴan sanda ya bada umarnin faɗaɗa bincike a kai.
You must be logged in to post a comment Login