Connect with us

Labarai

Ubandoma ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC

Published

on

Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Sokoto a zaɓen 2023, Mallam Sa’idu Umar Ubandoma, ya fice daga jam’iyyar  tare da komawa jam’iyyar APC.

 

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko kan yaɗa labarai, Bashar Abubakar, ya fitar, an ce Sanata Wamakko ne ya karɓi Ubandoma cikin APC a gidan sa da ke Asokoro,  a birnin tarayya Abuja.

 

Ubandoma, wanda ya taɓa zama Kwamishinan Kuɗi da Sakataren Gwamnatin Jihar Sokoto a zamanin gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya ce salon jagorancin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da ayyukan ci gaban da Gwamna Ahmed Aliyu ke yi ne suka ƙarfafa masa gwiwar komawa Jam’iyyar  ta APC.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!