Connect with us

Siyasa

Jam’iyyar hamayya ta ADC ta sanar da fara siyar da fom ɗin takara

Published

on

Jam’iyyar hamayya ta ADC ta sanar da fara siyar da fom ɗin takara muƙamai daban-daban gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

 

Hakan na kunshe cikin  sanarwar  da kakakin jam’iyyar na ƙasar,Malam  Bolaji Abdullahi ya fitar, da ta tabbatar da  jam’iyyar ta saka kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa akan naira miliyan 100.

 

Sanarwar ta kuma ce jam’iyyar ta fitar da jadawalin zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar, inda za a yi na shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Mayu.

 

Jam’iyyar ta kuma saka kuɗin fom ɗin takarar gwamna kan naira miliyan 50, yayin da na sanata ke naira miliyan 20, sai na ɗan majalisar tarayya a kan naira miliyan 10 da ɗan majalisar jiha naira miliyan uku.

 

Sanarwar ta kuma bayyana rangwamen kaso  50 cikin ɗari ga matasa, da ragin kaso  25 ga mata da masu buƙata ta musamman.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!