Connect with us

Labarai

Jam’iyyar NDC ta musanta labarin ficewar Kwankwaso daga cikin ta

Published

on

Jam’iyyar NDC ta musanta rahotannin da ake yadawa cewa ɗan takararta na mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar saboda saɓanin da ya taso kan rabon takara a Jihar Kano.

 

Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar NDC, na kasa Osa Director, ya bayyana cewa rahotannin ba gaskiya ba ne.

 

Director ya bayyana hakan a wata hira da tashar Talabijin ta Arise News, inda ya jaddada cewa Kwankwaso bai taɓa tunanin barin jam’iyyar ba.

 

Jami’in ya kara dacewa cewa ana samun saɓani a cikin jam’iyya sai dai hakan ba sabon abu ba ne a siyasa, musamman ga jam’iyyar da ke ƙoƙarin kara ƙarfi kafin babban zaɓen 2027.

 

Ya ce NDC za ta ci gaba da amfani da tattaunawa da sasanci wajen magance matsalolin cikin gida.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!