Kiwon Lafiya
Jam’iyyar PRP ta dakatar da shugaban jam’iyyar a Kano
Jam’iyyar PRP ta dakatar da shugaban jam’iyyar a nan Kano Sammani Sahrif da sakataren sa Bala Muhammad bisa zargin sa da aikata laifuka da dama da suka saba da dokikon jam’iyyar.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban zauren jam’iyyar na kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar nan Umar Tahir da aka rabawa manema labarai a yau Litinin.
Sanarwar ta ruwaito cewar shugaban yayi watsi da amfani da ofishin jam’iyyar na halaliya da ke kofar Mazugal, inda ya kirikiri wani ofishi na kashin kansa, trare da yin amfani da kudaden jam’iyyar aa’amuran da basu shafi jam’iyyar ba.
A don hakan ne kungiyar inuwar jam’iyyar ta bukaci ya bayyana a gaban kwamitin ladabtarwa a ranar Laraba mai zuwa da misalin karfe biyu na rana, yayin da kuma ake bukatar sakataran nasa ya bayyana a ranar Alhamis mai zuwa duka a harabar ofishin jam’iyyar da ke kofar mazugal.
Haka kuma jam’iyyar ta haramtawa dakataccen shugaban da kuma sakataren sa shiga kafafen yada labarai su magantu har sai an kammala bincike a kansu.