Connect with us

Labarai

Jarumar Kannywood Hawwa Maina ta rasu a asibitin koyarwa na Aminu Kano

Published

on

Fitacciyar jarumar shirin fina-finan kannywood Hauwa Maina ta rasu a asibitin koyarwa na Aminu Kano a daren larabar da ta gabata.

Marigayiya Hauwa Maina ta rasu ne sakamakon fama da ta yi da rashin lafiya ana kuma saran binne gawarta yau Alhamis a juhar Kaduna.

Hawwa Maina dai jaruma ce da ta yi fice a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, ta kuma lashe kyaututtuka a shekarar 2007 da 2010.

Marigayiya Hawwa Maina wadda ‘yar asalin garin Biu ce da ke jihar Borno an haifeta ne a garin Kaduna sannan ta yi karatun firamare a garin Geidam da da ke jihar Yobe da Kaduna, kafin daga bisani ta kammala karatun  Sakandire a Nguru da ke jihar ta jihar Yobe.

Haka zalika ta kuma yi karatun Diploma a bangaren gudanarwa a Kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic. Ta mutu ne ta bar ‘ya guda mai suna Maryam Bukar Hassan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!