Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Jin ƙai: Ganduje ya yafewa matar da ta kashe mijinta

Published

on

Gwaman Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yafewa wata mata Rahama Hussain da aka ɗaure da lafin kisan minjinta Tijjani Muhammad tun a shekarar 2015.

Rahma mai shekaru 20 ta samu ƴanci ne bayan da ta kwashe shekara shida ɗaure a gidan gyaran hali.

Tun a shekarar 2014 ne dai iyayen Rahma suka yi mata auren dole ga Tijjani Muhammad, lamarin da ya ƙara cusa ƙiyayyarsa a zuciyarta.

Ƙarin  Labarai:

Jinƙai: Babban jojin Kano ya sallami fursunoni

Ganduje ya gargadi fursunoni su guji aikata laifuka

Haka kuma a shekarar 2018 babbar kotun jiha ƙarƙashin mai shari’a R A Sadik, ta ce ta samu Rahma da lafin kisan kai dumu-dumu.

Sai dai mai shari’ar ya ce, Rahma ba ta balagaba, a don haka alhakin Gwamna ne ya yafe mata, ko kuma ta ci gaba da zama a gidan yari.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na gidan gyaran hali na Kano, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, Rahma ta shaƙi iskar ƴanci ne, bayan ziyarar da Gwamman ya kai gidan gayaran hali na Kurmanwa.

A yayin ziyarar ne kuma aka roƙi Gwamnan da ya yafe mata, bayan da aka tabbatar ta yi nadama ta kuma nuna halaye na gari.

Wannan ce ta sanya Gwamman ya yafe mata, ya kuma yi alƙawarin ɗaukar nauyin karatunta.

Sai dai an kasa samun wani jawabi daga bakin Rahma, illa kuka da godiya ga Gwamman da ya yafe mata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!