Connect with us

Labarai

Jirgi na biyu na maniyyatan Jigawa zai tashi a yau

Published

on

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa, ta ce, Jirgi na biyu na maniyyatan jihar zai tashi a yau Talata bayan tashin jirgin farko dauke da maniyyata 480 zuwa kasa mai tsarki a jiya Litinin.

 

Shugaban hukumar jin dadin alhazai Alhaji Ahmad Umar Labbo ne ya bayyana haka ga wakilinmu Freedom Radio Dutse Aminu Umar Shuwajo.

 

Haka kuma, shugaban ya jaddada kudirin hukumar bisa sahalewar gwamna Malam Umar Namadi, na tabbatar da bai wa kowane  maniyyaci abinci sau uku a kowace rana ciki har da nau’in abincin masu fama da larurar ciwon suga.

 

Maniyyata 899 ne ake sa ran za su sauke farali bana a jihar ta Jigawa, wadda tini jirin farko ya sauka a birnin Madina tun a jiya Litinin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!