Connect with us

Labarai

Yan Sanda sun bayyana damuwa kan karuwar shaye-shaye a Gombe

Published

on

Rundunar yan Sandan Najeriya, ta bayyana damuwa kan yadda shaye-shayen miyagun kwayoyi da ta’addancin siyasa ke karuwa a jihar Gombe, ta na mai cewa abubuwa ne masu alaƙa da juna da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya musamman yayin da zabe ke gabatowa.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Gombe, Umar Chuso, ya bayyana haka a wani taron wayar da kai da aka gudanar a jihar.

 

Ya bayyana cewa shaye-shayen kwayoyi na jefa matasa cikin aikata laifuka, yayin da ‘yan siyasa marasa kishin kasa ke amfani da matasa masu rauni wajen tayar da fitina.

 

Ya kara da cewa wannan yana haifar da rashin tsaro, don haka ya bukaci al’umma su rika ba da bayanan sirri da kuma gina amana tsakanin jama’a da ‘yan sanda domin hana aikata laifuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!