Labarai
Jonathan ya buƙaci jam’iyyu da bangaren shari’a sauke nauyin da ke kansu na kare Dimokuraɗiyya

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da bangaren shari’a da su sauke nauyin da ke kansu wajen kare dimokuraɗiyya a Afirka.
Jonathan ya yi wannan magana ne a taron Goodluck Jonathan Foundation Democracy Dialogue 2026 da aka gudanar a Bauchi, inda ya ce jam’iyyun siyasa su fifita muradun kasa, yayin da kotuna za su kasance masu cin gashin kansu da bin doka.
Ya ce karfafa dimokuraɗiyya na bukatar sahihin zabe, bin doka, kare hakkin jama’a, rarraba madafun iko da tabbatar da gaskiya da rikon amana.
You must be logged in to post a comment Login