Labarai
Kadan ya rage mu kawo karshen matsalolin tsaro – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnonin Arewa da su tattauna tare da kirkiro hanyoyin hadin gwiwa da jami’an tsaro da kuma jama’a, domin kawar da ta’addanci da matsalolin tsaro a yankunan.
Buhari ya bayyana haka ne a yau Alhamis 25 ga watan Fabrairu yayin taron kungiyar gwamnonin Arewa da aka gudanar a jihar Kaduna, ya kuma samu halartar shugabannin majalisar sarakunan arewacin kasar nan.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya da ya wakilci shugaban kasa, Ibrahim Gambari, ya ce, gwamnatin tarayya za ta cigaba da magance ayyukan masu tada kayar baya da ‘yan fashi da masu satar mutane da kuma sauran masu laifi da ke zama barazana ga yan kasa nagari.
Haka kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmai Muhammadu Sa’ad, ya ce, “Za mu cigaba da marawa gwamnonin baya, ina kuma jinjina ga gwamnonin na arewa da suka je wuraren da matsalolin tsaro suka faru don jajantawa tare da tsayawa don ganin mutanen arewa su samu karbuwa a wuraren.”
You must be logged in to post a comment Login