Labarai
Kaduna: Yan sanda sun kama mutane 41 da ake zargi da garkuwa da mutane da fashi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama mutane 41 da ake zargi da garkuwa da mutane da fashi da makami, sannan ta ceto mutane bakwai da aka kashe tare da kwato makamai da shanu da aka sace a wani samame da ta kai a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar , Rabiu Muhammad, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai.
Ya kuma ce an samu nasarori tsakanin watan Maris da wannan watan na Aprilu ta hanyar jami’an tsaro da kuma samun baya nan sirri.
Kazalika ya ce rundunar ta kuma kwato makamai 24, harsasai 200 da kuma shanu 50 da aka sace. a jihar.
You must be logged in to post a comment Login