Connect with us

Kaduna

Kaduna: Matashi ya rasa ransa a harin ƴan bindiga a Rigasa

Published

on

Rahotanni sun ce da misalin ƙarfe 8 na dare ne gun-gun ƴan bindigar suka je unguwar ta Rigasa dab da tashar jirgin ƙasa.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan jihar Kaduna ASP. Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce, ƴan sanda sun je wurin har ma sun yi musayar wuta wanda daga bisani ƴan ta’addar suka arce.

Jalige ya ce, wani matashi mai suna Rabi’u Auwal ya rasa ransa sanadiyyar harbi a yayin faruwar lamarin.

Kafin rasuwarsa Rabi’u Auwal na cikin matasan arewa masu fafutukar yaƙi da rashin tsaro.

Jihar Kaduna dai na cikin jihohin da matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara.

Ko a makon da ya gabata wasu ƴan bindiga sun kutsa kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli inda suka yi garkuwa da daliabi, sai dai yan bindigar sun bukaci kudin fansa da ya kai naira miliyan 270.

Kuma har kawo wannan lokaci ba a samu kuɓutar da su ba.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 334,910 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!