Labarai
Kaduna : muna garkame makaratun da suka ki yin bibiya da umarnin mu
Maaikatar ilimin jahar Kaduna ta bibiyi wasu daga cikin makarantun kudin da ta samu labarin cewa basu bi umarnin da maaikatar ta bayar ba na cewa a garkame makarantun jahar daga ranar litinin 23 ga watan Maris din nan har sai nan da kwana talatin.
Batun garkame makarantun dai ya biyo bayan bullar balahirar cutar nan ne na KORONA VIRUS (covid 19) a cewar sa kwamishinan ilimin jahar Shehu Muhammed Makarfi sun dauki matakin garkame makarantun ne dan takaita yaduwar cutar duk da ba a samu bullar cutar a jahar ba, a cewar sa matakan kariya ne kawai ake dauka.
A nata bayanin daraktar dake kula da ingancin makarantu a jahar Umma K. Ahmad wacce ita ce ta jagoranci tawaga dan tabbatar da makarantu sun bi dokar da aka basu tace basu kama Ko da makaranta guda daya na gudanar koyarwa ba.
“mun samu labarin cewa makarantu na ci gaba da karatu a makarantun su, sai dai kafin muzo sun kulle, dama kuma abunda muke so ke nan”
Daga karshe ta shawarci iyayen yara da su sanya ido akan yayan su yanda ya kamata musamman ma wajen killace yayan su a gida da kuma bin dokokin da jamian lafiya suka bayar da tabbatar da yaran sun bi dokar.
You must be logged in to post a comment Login